Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe 'yan ta'adda 80 yayin musayar wutar sojoji a arewacin Burkina Faso
2019-12-25 13:14:10        cri

Hukumar tsaron kasar Burkina Faso ta sanar da cewa, dakarun sojojin kasar sun hallaka 'yan ta'adda 80 yayin wani kazamin harin da 'yan ta'addana suka kaiwa sansanin sojojin da fararen hula a yankin Arbinda da ke lardin Soum, rundunar sojojin kasar Burkina Faso ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

A cewar sanarwar, da sanyin safiyar Talata ne, wasu gungun mayakan 'yan ta'adda suka kaddamar da kazamin hari kan sansanin sojojin da fararen hula dake yankinn Arbinda a lardin Soum, inda dakarun sojojin Burkina Faso suka samu nasarar kashe 'yan ta'adda 80.

Sai dai kuma, a lokacin arangamar, an kashe jami'an tsaro 7, wanda ya kunshi sojoji 4, da 'yan sanda 3, kana an jikkata mutane sama da 20.

Rundunar sojojin Burkina Faso ta kuma tabbatar da mutuwar fararen hula sai dai ba ta bayyana hakikanin adadinsu ba. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China