Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi tir da harin da aka kai Burkina Faso
2019-11-08 11:16:46        cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harin da aka kai kan jerin gwanon motocin wani kamfanin hakar ma'adinai a Burkina Faso, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane da raunata wasu da dama.

Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ruwaito Antonio Guterres na yin kira ga hukumomin kasar, su yi dukkan mai yiyuwa na tabbatar da hukunta wadanda suka aiwatar da wannan mummunan aiki a kan fararen hula.

Antonio Guterres ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka mutu da gwamnatin Burkina Faso, sannan ya yi wa wadanda suka raunata fatan samun lafiya cikin sauri.

Sakatare Janar din ya kuma jaddada cikakken goyon MDD ga gwamnatin Burkina Faso, yayin da take ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China