Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe yan ta'adda 32 yayin wani gumurzu a arewacin Burkina Faso
2019-11-18 11:41:44        cri
Rundunar sojin Burkina Faso, ta ce an kashe 'yan ta'adda 32 yayin wani gumurzu a ranar Juma'a, a yankunan tsakiya maso arewa da kuma arewacin kasar.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce 'yan ta'adda 24 sun rasa rayukansu ne yayin wata kwantar bauna da sojoji masu sintiri suka yi musu a yankin Yorsala na Titao dake lardin Loroum na arewacin kasar, yayin da aka kashe sauran 8 a yankin Bourzanfa na lardin Bam dake tsakiya maso arewacin kasar.

Sanarwar ta ce bisa sahihan bayanai da aka samu, jami'an tsaron yankin arewacin kasar sun kuma kaddamar da farmaki a yankin Bourzanga dake tsakiya maso arewacin kasar, a ranar Asabar.

Burkina Faso na fama da tabarbarewar yanayin tsaro a yankunan arewacin kasar, wadanda ke fama da hare-haren 'yan ta'adda.

Tun daga shekarar 2015, ayyukan 'yan ta'adda sun yi sanadin mutuwar mutane sama da 500 cikin har da jami'an tsaro 200, tare kuma da raba dubban jama'a daga matsugunansu a kasar ta yammacin Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China