![]() |
|
2019-10-13 15:20:37 cri |
Harin an kaddamar da shi ne da yammacin Juma'a a kauyen Salmossi na lardin Oudalan dake arewacin kasar, sai dai ba'a samu rahoton ba sai a ranar Asabar.
Sakatare janar din ya bayyana sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da gwamnati, da ma al'ummar kasar ta Burkina Faso. Kana ya yi fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka samu raunuka, kakakin babban sakataren Stephane Dujarric, shi ne ya bayyana cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta ce babban sakataren ya jaddada aniyar MDD na yin aiki tare da kasar Burkina Faso wajen kyautata yayin zaman rayuwar al'ummma, da kuma tabbatar da dora kasar kan shirin samar da dauwwammamen ci gaba.
Tun da farko a ranar Asabar, shugaban gamayyar Alliance of Civilizations na MDD, Miguel Angel Moratinos, shi ma ya yi Allah wadai da harin. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China