Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Burkina Faso sun yi bikin murnar cika shekaru 59 da kafuwarsu duk da kalubalolin tsaro
2019-11-03 16:31:59        cri
Rundunar sojojin kasar Burkina Faso ta gudanar da bikin murnar cika shekaru 59 da kafuwarta duk da yawaitar barazanar ta'adanci da makamantan hare-hare dake addabar kasar ta yammacin Afrika.

An gudanar da bikin ne a ranar Juma'a mai taken "Kawance mai girma ta al'ummomin kasa da rundunar sojojin kasar wadda ke yakar ta'addanci".

Ministan tsaron kasar Shérif Sy ya bayyana cikin jawabin da ya gabatar cewa, ba za su taba yin kasa a gwiwa ba, ko nuna gazawa ko kuma mika wuya ga duk wata barazana ba.

Ya ce mutuwar zuciya ba za ta taba samun gindin zama a zukatan sojojin kasar Burkina Faso ba.

An gabatar da bikin wanda ya samu halartar shugaban kasar Burkina Fason Roch Marc Christian Kaboré.

Kasar Burkina Faso tana fuskantar matsanancin yanayin tabarbarewar tsaro, galibi a shiyyar arewacin kasar, kusan a kullum ana samun hare haren ta'addanci wadanda ke jefa fargaba ga zukatan jama'ar kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China