Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A kalla mutane 37 suka rasu wasu 60 suka jikkata yayin wani kwantan bauna a gabashin Burkina Faso
2019-11-07 19:52:01        cri
Gwamnan lardin Tapoa dake gabashin Burkina Faso Saïdou Sanou, ya tabbatar da rasuwar mutane akalla 37 ciki hadda wasu sojojin kasar, baya ga wasu 60 da suka jikkata, yayin wani kwantan bauna da wasu mahara suka yi musu a jiya Laraba.

Gwamnan ya ce, mutanen da harin ya rutsa da su, na cikin wani jerin gwanon motoci ne masu dauke da 'yan kwadagon kamfanin Semafo na kasar Canada, dake aikin hakar ma'adanai, wadanda kuma wasu sojojin kasar ke yiwa rakiya. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China