Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe 'yan ta'adda 28 a hare haren da sojoji suka kaddamar a arewacin Burkina Faso
2019-12-07 16:20:39        cri
Kimanin mayakan 'yan ta'adda 30 ne sojojin kasar Burkina Faso suka hallaka a wasu hare haren da suka kaddamar ta jiragen sama a ranar Laraba, a shiyyar arewacin kasar mai fama da tashin hankali, kafafen yada lanbaran kasar sun ba da rahoton kamar yadda wasu majiyoyin daga hukumomin tsaron kasar suka bayyana.

A cewar majiyoyin, an kaddamar da haren a ranar Laraba a yankunan Tiawbal, da Kain, da kuma Yense dake shiyyar arewacin lardin Yatenga.

Rahotannin sun ce, an hallaka 'yan ta'adda 28 tare da lalata wasu injina da wajen ajiye man fetur mallakar 'yan ta'addan.

A cikin 'yan makonnin da suka gabata, sojojin Burkina Faso suka zafafa shirin kaddamar da wasu munanan hare hare ta sama da ta kasa domin fatattakar mayakan 'yan ta'addar dake addabar kasar tun daga shekarar 2015.

Tun daga shekarar ta 2015, kasar Burkina Faso ke cigaba da fuskantar hare haren 'yan ta'adda, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe rayukan sama da mutane 500, kana sama da rabin miliyan suka tsere daga muhallansu, wadanda suka hada da kananan yara sama da 9,000. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China