Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin kwararru na AU ya nuna damuwa game da karuwar ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi a Afrika
2019-12-25 13:07:24        cri

Kwamitin kwararru masu ilmin tabbatar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afrika (AU), ya bayyana matukar damuwa game da karuwar ayyukan ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi a sassa daban daban na nahiyar Afrika.

A sanarwar da ya fitar a ranar Talata, kwamitin na AU ya ce, matsalolin ayyukan ta'addanci da na masu tsattsauran ra'ayi yana ci gaba da ta'azzara a galibin yankunan Afrika, matsalolin suna matukar haifar da mummunar illa ga zaman rayuwar jama'a da kuma barnata dukiyoyi masu dimbin yawa.

Sanarwar da kungiyar mai mambobin kasashen Afrika 55 ta fitar, kwamitin ya damu matukar game da illolin da matsalar ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi ke haifarwa ga rayuwa jama'a da barnata dukiyoyi, musamman a yankunan Sahel, da tafkin Chadi, da kuma gabashin Afrika inda matsalar ta fi Kamari.

Bugu da kari sanarwar ta ce matsalar tana ci gaba da yaduwa cikin sauri a wasu yankunan Afrika musamman shiyyar yammaci, tsakiya, da kudancin Afrika. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China