Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Afirka: Makamashi mai tsafta shi ne ginshikin samar da tsaron abinci
2019-12-20 08:50:46        cri

Kungiyar masana aikin gona da muhallin halittu mai suna "Malabo Montpellier Panel" ta bayyana a cikin wani rahoto da ta fitar mai taken "Sa kaimi: manufofin kirkire-kirkire da za su farfado da tsarin aikin gona da samar da abinci na Afirka" cewa, samun makamashi mai tsafta shi ne zai inganta matakan kawar da talauci da yunwa da abinci mai gina jiki a nahiyar.

Da yake karin haske, shugaban kungiyar Ousamane Badiane, ya bayyana cewa, samun makamashi mai araha kuma mai dorewa da zai kai ga share gonaki, da shuka amfani gona, da girbi, da sarrafa shi, da raba shi har ma a kai ga dafa shi, za su tabbatar da biyan bukatun bangaren aikin gonar nahiyar, a fannin sauyin yanayi da karancin albarkatun kasa.

A cwar rahoton, a shekarar 2018 kimanin iyalai miliyan biyar a nahiyar ta Afirka sun kafa faranten samun wuta daga hasken rana, lamarin da ya bunkasa ajandar nahiyar na kare muhalli.

Rahoton ya ce, nahiyar tana bukatar jarin da ya kai dala biliyan 120 a kowa ce shekarar har zuwa shekarar 2040, kafin ta cimma burinta na samun makamashin bai daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China