Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Macron ya lashi takobin yaki da masu tsattsauran ra'ayi na IS a yammacin Afrika
2019-12-22 16:51:02        cri
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sha alwashin cigaba da yakar tsattsauran ra'ayi na kungiyar (IS) a yammacin Afrika, kalaman na Macron na zuwa ne bayan da sojojin Faransa suka yi nasarar hallaka mayakan kungiyar IS masu da'awar kafa daular musulunci kimanin 33 a kasar Mali a farkon wannan rana.

Ya ce, "Tilas ne a tsaya tsayin daka kuma a hada kai domin tinkarar kalubalolin da ake fuskanta," Macron, wanda a halin yanzu ya shiga rana ta biyu na ziyarar aikin da ya kai yammacin Afrika, ya fada a lokacin taron manema labarai a birnin Abidjan na kasar Kwadebuwa cewa, zasu cigaba da yakin.

Dakarun sojojin Faransa suna gudanar da ayyukan wanzar da tsaro ta hanyar amfani da jiragen sama masu saukar ungulu, da sojojin kasa, da kuma jirage marasa matuka a yankin Mopti dake shiyyar tsakiyar Mali.

Tun a shekarar 2015, kimanin dakarun sojoji 4,500 Faransa ta tura zuwa yankin Sahel na yammacin Afrika domin fatattakar mayakan kungiyar masu tsattsauran ra'ayi da kuma maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China