Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Afrika za su yi hadin gwiwar moriyar juna don ta zama abin misali a duniya
2019-12-22 16:19:07        cri
Wani babban jami'in gwamnatin kasar Sin ya bayyana cewa kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen Afrika domin kafa wani tsarin hadin gwiwar da zai amfanawa dukkan bangarorin ta yadda zai kasance abin misali tsakanin kasashe masu tasowa.

Yang Jiechi, mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC), shine ya bayyana hakan a yayin da yake kammala ziyarar aikinsa a kasashen Uganda, jamhuriyar Kongo da kuma Senegal.

Yang, wanda kuma shi ne daraktan ofishin hukumar hulda da kasashen waje ta kwamitin JKS, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ya gana da shugabannin kasashen uku kuma ya tattauna da ministocin harkokin wajen kasashen, inda suka cimma matsaya da juna.

Mista Yang yace, kasar Sin, ta kasance kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kana Afrika itace nahiyar dake da kasashe masu tasowa mafi yawa a duniya, bangarorin biyu suna tallafawa juna da yin hadin gwiwa ta kut-da-kut da juna game da al'amurran kasa da kasa.

Ya kara da cewa, shekarar 2020 za'a yi bikin cika shekaru 20 da kafuwar dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato (FOCAC), yace kasar Sin zata yi aiki tare da kasar Senegal a matsayin jagora, tare da sauran kasashen Afrika domin yin musayar ra'ayoyi da kuma kara zurfafa hadin gwiwa kan shawarar ziri daya da hanya daya.

Tun bayan kafa dandalin FOCAC a watan Oktoban shekarar 2000, an gudanar da taron ministoci sau 7 da kuma taron koli 3, ya zama tilas a yabawa kokarin kasashen Sin da Afrika.

Ya ya ce, "duk wuya duk rintsi, kasar Sin zata cigaba da nacewa kan mu'amalarta da kasashen Afrika, kafada da kafada kuma hannu da hannu, domin ciyar da abokantakar dake tsakanin bangarorin biyu gaba".

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China