Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen yammacin Afrika sun sauya sunan kudin bai daya na shiyyar
2019-12-22 17:00:36        cri
Wani al'amari da shugaban kasar Kwadebuwa Alassane Ouattara ya bayyana a matsayin mai cike da tarihi shi ne, yadda kasashen yammacin Afrika 8 suka sauyawa kudin bai daya na shiyyar suna daga CFA franc, zuwa "Eco".

Ouattara yayi tsokacin ne a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a birnin Abidjan, yayin da suke tare da shugaban kasar Faransa Macron.

Kasashen Afrika takwas, da suka hada da Benin, Burkina Faso, Guinea-Bissau, Kwadebuwa, Mali, Nijer, Senegal da Togo, zasu dinga amfani da sabon kudin na bai daya. Dukkan kasashen sun taba kasancewa karkashin renon Faransa ne in banda Guinea-Bissau.

Kasashen sun fara amfani da kudin na CFA tun a shekarar 1945, a wancan lokacin suna karkashin mulkin mallakar Faransa, wanda aka fi sani da "kasashen Afrika renon Faransa". Masu adawa da kudaden sun bayyana cewa har yanzu bata sauya zane ba game da mulkin mallakar Faransa yayin da masu goyon baya suna cewa tsarin ya samar da kyakkyawan ingancin tafiyar da al'amurran kudade a shiyyar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China