Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Amurka sun cimma matsaya kan yarjejeniyar cinikayya bisa mataki na farko
2019-12-14 08:53:06        cri

Rahotannin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin kasar Sin wato CMG a takaice sun nuna cewa, kasashen Sin da Amurka sun riga sun cimma matsaya kan takardun yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya bisa mataki na farko, takardun dake kunshe fannoni tara wato gabatarwa, da ikon mallakar fasaha, da sayar da fasahohi, da abinci da amfanin gona, da hidimar hada-hadar kudi, da darajar musanyar kudi, da habaka cinikayyar bangarorin biyu, da yi wa juna kimantawa, da daidaita rikicin dake tsakanin sassan biyu, da kuma yarjejeniya ta karshe. A sa'i daya, sassan biyu sun cimma matsaya cewa, Amurka za ta cika alkawarin soke matakan kara haraji ga kayayyakin kasar Sin da take shigo da su kasar bisa matakai daban daban, har za ta rage harajin a kai a kai.

Yarjejeniyar da suka cimma za ta taimaka kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, haka kuma za ta taka rawa kan bincike da daidaita sabanin dake tsakanin sassan biyu wajen tattalin arziki da cinikayya, har za ta ingiza ci gaban huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka cikin lumana, musamman ma a halin da ake ciki yanzu wato tattalin arzikin duniya bai gudana yadda ya kamata ba, yarjejeniyar da sassan biyu suka cimma za ta kara karfin kasuwar kasa da kasa, tare kuma da samar da wani muhallin tattalin arziki da cinikayya da zuba jari a fadin duniya.

Kana Sin da Amurka sun yi alkawarin cewa, nan gaba za su yi hanzari domin kammala wajababbun ayyukan bincike da fassara da gyarawa tun da wuri, kana za su yi tattaunawa kan batun game da hakikanin lokacin da za su daddale yarjejeniyar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China