Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban taron MDD ya amince da takardun hadin gwiwa na taron BRF karo na 2 a matsayin takardun MDD
2019-05-25 16:15:48        cri

Babban taron MDD, ya amince a jiya, da jawabin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar yayin bikin bude taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa dangane da shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na 2 da kuma sanarwar hadin gwiwar da aka cimma yayin taron, a matsayin takardun MDD a hukumance, inda aka rarraba su tsakanin mambobin majalisar.

Daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Afrilun bana ne aka gudanar da taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa dangane da shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na 2 a nan Beijing. Babban taken taron shi ne "aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya', a kokarin samun kyakkyawan makoma". (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China