Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan cinikin waje na Sin a watanni 9 na farkon bana ya karu da kashi 2.8 cikin dari
2019-10-14 13:55:33        cri
Bisa kididdigar da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar a yau, an ce, yawan kudin cinikin shigi da fici na kasar Sin a watanni 9 na farkon bana ya kai Yuan biliyan 22910, wanda ya karu da kashi 2.8 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, hakan ya nuna samun karuwa a wannan fanni.

Kakakin babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Li Kuiwen ya bayyana a gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar a yau cewa, cinikin waje na kasar Sin ya kara taka muhimmiyar rawa wajen raya dukkan cinikin kasar, kana an kara samun fadaduwar kasuwa, da inganta karfin kamfanonin kasar masu zaman kansu na yin cinikin waje.

Yawan cinikin waje na kasashe wadanda suke aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" yana ci gaba da samun karuwa. Yawan kudin cinikin shigi da fici a tsakanin Sin da wadannan kasashe a watanni 9 na farkon bana ya kai Yuan biliyan 6650, wanda ya karu da kashi 9.5 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, kana yawansu ya kai kashi 29 cikin dari bisa adadin cinikin waje na kasar Sin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China