Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya mika sakon murna ga bikin baje kolin hada-hadar cinikayya ta yanar gizo
2019-10-11 13:59:25        cri
Yau Jumma'a, an bude bikin baje kolin hada-hadar cinikayya ta yanar gizo na kasa da kasa a birnin Shijiazhuang dake lardin Hebei na kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon murnar bude wannan biki.

Shugaba Xi ya ce, a halin yanzu, ana samun bunkasuwar kimiyya da fasaha cikin sauri, hada-hadar cinikayya ta yanar gizo tana kuma bunkasuwa cikin yanayi mai kyau, lamarin da ya canja zaman rayuwar al'umma, yayin da ya yi tasiri kan ci gaban tattalin arziki, da yadda ake gudanar da harkokin kasa da kasa, da kuma ci gaba na al'adun bil Adama.

Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana mai da hankali kan raya hada-hadar cinikayya ta yanar gizo, tana kuma dukufa wajen hada hada-hadar cinikayya ta yanar gizo da hada-hadar cinikayya da ba ta yanar gizo ba tare, bisa sabbin ka'odojin sabuntawa, daidaituwa, kiyaye muhalli, bude kofa da kuma cin gajiya tare, ta yadda za a iya raya tattalin arziki yadda ya kamata. Ya kuma nuna fatan zurfafa musayar ra'ayoyi a tsakanin mahalarta bikin, don su tattana yadda za a iya raya hada-hadar cinikayya ta yanar gizo da kyau, domin tallafawa al'ummomin kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China