Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yang Jiechi ya gana da shugaban kasar Uganda
2019-12-19 10:52:15        cri
Jiya Laraba, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, kana darektan ofishin kwamitin kula da harkokin wajen kasar Sin, Yang Jiechi ya gana da shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni a fadar shugaban kasa dake birnin Entebbe.

A yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya ce, bisa jagoranci na shugabannin kasashen biyu, an kyautata dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Uganda zuwa dangantakar abokantaka bisa dukkan fannoni, wato, huldar dake tsakanin kasashen biyu ta shiga yanayi mafi kyau cikin tarihin alakar kasashen biyu. Sabo da haka, an cimma sakamako da dama bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, kana kasashen biyu za su ci gaba da zurfafa fahimtar juna a tsakaninsu, suna kuma goyon bayan juna kan harkokin dake janyo hankulansu, da karfafa hadin gwiwarsu kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Ya ce, a nan gaba, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Uganda wajen aiwatar da ra'ayoyin da shugabannnin biyu suka cimma, da sakamakon da aka samu a taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing, domin zurfafa hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin ciniki, makamashi, yankunan masana'antu da ababen more rayuwa da dai sauransu.

A nasa bangare, shugaba Museveni ya ce, a halin yanzu, ya kamata nahiyar Afirka mai wayewar kai ta gaggauta aikin raya harkokin masana'antu na zamani, kuma tana bukatar taimako da fasahohin kasar Sin wajen cimma wannan buri. Kasar Uganda tana son habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, domin ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China