Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yang Jiechi ya gana da shugabannin tawagogin wakilan Afrika a Beijing
2019-06-25 11:04:36        cri
Mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin, kana direktan ofishin kwamiti mai kula da harkokin waje na kwamitin tsakiyar, Yang Jiechi, ya gana da shugabannin tawagogin wakilan Afrika, da suka halarci taron tabbatar da nasarorin da aka samu a taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika, a jiya Litinin a nan birnin Beijing.

Yayin ganawar tasu, Mista Yang ya ce, Sin na fatan hadin kai da kasashen Afrika, don yin amfani da wasu damammaki masu kyau na tabbatar da nasarorin da aka samu a taron kolin da raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", ta yadda za su kara kawo moriyar juna da samun bunkasuwa tare, da habaka hadin gwiwarsu, da kara tuntubar juna da yi koyi da juna, kana da kara yin musanyar ra'ayi kan wasu manyan batutuwa na shiyya-shiyya da na kasa da kasa dake jan hankalinsu gaba daya, har ma da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga al'ummar Sin da Afrika.

Ministan harkokin wajen kasar Senegal Amadou Ba, wadda kasa ce dake rike da shugabancin tawagogin Afrika na dandalin, ya ce, muhimmin abun dake jawo hankalinsu shi ne, dandali ya dauki wasu matakai masu yakini, matakin da ya dace da muradun jama'ar Afrika kwarai da gaske. Ban da wannan kuma, Afrika da Sin na zama gefe daya kan wasu manyan batutuwa na kasa da kasa, taron a wannan karo dai, zai kai ga cimma matsaya daya tsakanin bangarorin biyu don kara hada kansu da nacewa ga manufar gudanar da harkokin duniya tsakanin bangarori daban-daban. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China