Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taro mai muhimmancin gaske na Sin da FAO
2019-11-29 16:34:54        cri
An gudanar da taro mai muhimmancin gaske na cika shekaru 10 da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa a tsakanin kasar Sin da hukumar kula da abinci da aikin noma ta MDD wato FAO, tsakanin ranekun 25 zuwa 26 ga wannan wata a birnin Kampala na kasar Uganda.

Taken taron a wannan karo shi ne "Yi hangen nesa kan makomar hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa da bangarori uku, ta hanyar sa kaimi da fahimtar juna da yin kirkire-kirkire". A yayin taron, Sin da Uganda, da hukumar FAO, sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwar dake tsakaninsu.

A yayin bikin budewar taron, shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni ya yi jawabi, inda ya yi godiya ga kasar Sin domin ta samar da gudummawa ga kasar Uganda wajen yaki da talauci bayan samun 'yancin kai, kana ya gabatar da shawarwari kan yadda za a yi amfani da dandanlin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, don sa kaimi ga zuba jari da yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Uganda.

A nasa bangare, direktan hukumar FAO Qu Dongyu, ya mika wasikar murna ga taron, inda ya nuna yabo ga kasar Sin, bisa samar da gudummawa wajen cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa kafin shekarar 2030. Kana ya yi fatan bangarori daban daban za su kara yin hadin gwiwa don fadada dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare ta hanyar amincewa da bambance-bambance da ke tsakanin su. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China