Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Uganda ta kafa kwamitin da zai duba damammakin kasuwa da kasar ke da su bayan rattaba hannu a yarjejeniyar AfCFTA
2019-08-21 09:15:20        cri
Kasar Uganda ta kafa wani kwamiti na musamman, wanda zai duba damammakin kasuwa da kasar ke da su a sassan nahiyar Afirka, bayan da kasar ta rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta nahiyar ko AfCFTA a takaice.

Da yake karin haske game da hakan gaban 'yan majalissar dokokin kasar, ministan ma'aikatar cinikayya, masana'antu da jam'iyyun gama kai na kasar Amelia Kyambadde, ya ce kwamitin zai duba damammakin takara da Uganda ke da su a kasuwannin Afirka, domin tabbatar da moriyarta a kasuwannin nahiyar.

Ya ce karkashin wannan yarjejeniya, Uganda za ta iya cin gajiya ta fadadar kasuwa, da bunkasa fannin sarrafa kayayyaki, da cinikayya da samar da karin guraben ayyukan yi.

Ministan ya kara da cewa, Uganda na fatan cin gajiya daga cinikayyar dabbobin kiwo, da Gahawa, da ganyen shayi, da karafa, da dai sauran su. A bangaren ba da hidima kuma, tana iya cin gajiya daga sashen ilimi, da yawon bude ido, da hada hadar kasuwanci da samar da ababen more rayuwa.

Kyambadde ya ce, Uganda na fatan fadada kasuwar ta a kasashen Najeriya, da Ghana, da Kamaru, da Morocco, da Algeria da kuma Tunisia. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China