Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An tabbatar da samun rahoton Ebola na biyu a yammacin Uganda
2019-08-30 13:32:02        cri

Ma'aikatar lafiyar kasar Uganda ta sanar a jiya Alhamis cewa, an samu rahoton kamuwa da annobar cutar Ebola karo na biyu a yammacin gundumar Kasese, mai tazarar kilomita 472 daga Kampala, babban birnin kasar, tun bayan da aka samu barkewar annobar cutar daga makawabciyar kasar jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC).

Joyce Moriku Kaducu, ministar kula da lafiya matakin farko ta kasar, ta fada cikin wata sanarwa cewa, wata yarinya 'yar shekaru 9 da haihuwa 'yar asalin kasar Kongo, wacce ta shiga kasar tare da mahaifiyarta a ranar Laraba ta kan iyakar Mpondwe domin neman magani a asibitin Bwera, an tabbatar da gwajin da aka yi mata tana dauke da kwayar cutar mai saurin kisa.

Ministar ta ce, saboda an riga an gano yarinyar a hanyarta ta shiga kasar Uganda, babu wani mutum da ta yi mu'amala da shi a Ugandan. Ana ba ta magani ne a cibiyar shawo kan cutar Ebola da aka kafa a Kasese.

A watan Yunin bana, Uganda ta tabbatar da cewa, akwai wadansu mutane uku da ake kyautata zaton suna da alamun cutar, bayan da suka ziyarci jamhuriyar Kongo. An bayyana dakile cutar bayan an kammala kula da su na tsawon kwanaki 42, tun bayan da aka killace su.

Moriku ta ce, tuni aka tura wata tawagar ba da agajin gaggawa zuwa Kasese a jiya Alhamis domin taimakawa gundumar, wajen gudanar da ayyukan da kula da al'umma, da gano wadanda ake zaton an yi mu'amala da su, da yin rigakafin cutar da dai sauransu.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China