Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manzon musamman na shugaban kasar Sin ya gana da shugaban kasar Saliyo
2019-09-07 16:30:24        cri

Manzon musamman na shugaban kasar Sin, Yang Jiechi, jiya Juma'a ya gana da shugaban Saliyo, Julius Maada Bio a Freetown, fadar mulkin kasar.

Yayin ganawar, Yang Jiechi ya ce, Sin na fatan hadin kai da Saliyo bisa tsarin dandalin tattauna hadin kan Sin da Afrika, ta yadda za su gaggauta hadin gwiwarsu a fannonin raya manyan ababen more rayuwa da aikin gona da kiwon kifi da kiwon lafiya da ilmi da horaswa da dai sauransu, matakan da za su amfanawa jama'ar bangarorin biyu.

A nasa bangaren, shugaba Julius Maada Bio, ya taya kasar Sin murnar cika shekaru 70 da kafuwa, kuma ya jinjinawa ci gaba mai armashi da kasar Sin ta samu a fannonin tattalin arziki da zaman takewar al'umma, kana ya yi godiya sosai ga taimakon da Sin din ta dade tana ba kasarsa. Ya ce, Saliyo na maraba da shawarar "Ziri daya da hanya daya" da tunanin raya kyakkyawar makomar Bil Adam ta bai daya da shugaba Xi Jinping ya gabatar. Haka zalika, Saliyo na fatan zurfafa hadin kai da cin moriya da kasar Sin, da kara fahimtar juna kan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya tsakaninsu, bisa tsarin dandalin tattauna hadin kan Sin da Afrika, ta yadda za a ingiza ci gaban dangantakar kasashen biyu zuwa gaba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China