Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a iya amfani da dabarun shugabanci na kasar Sin a Afrika
2019-08-31 16:42:35        cri

Mataimakin Sakatare Janar na jam'iyyar Uganda's National Resistance Mov't Richard Todwong, ya ce kasashen Afrika za su iya amfani da nasarorin da kasar Sin ta samu a gogewarta a harkar shugabanci.

Yayin wata hira da aka yi da shi a baya bayan nan, Richard Todwong ya ce ya yi amanna, dabarun shugabanci da suka mayar da hankali kan kyautata zaman rayuwar jama'a da yaki da cin hanci, za su bunkasa tattalin arzikin kasa, yana mai cewa hidimtawa jama'a, shi ne jigon samun ci gaban zaman takewa.

Ya ce kasar Sin ta yaki cin hanci ta fuskoki da dama. Kana ya kara da cewa, toshe duk wata kafa da rarar arzikin gwamnati ke zurarewa, da tabbatar da duk wani arzikin gwamnati ya amfanawa kowa cikin adalci, da gargadi ko tsarewa ko korar masu almubazzaranci daga aikin gwamnati, za su samar da ci gaban zaman takewar al'umma idan aka aiwatar da su yadda ya kamata.

Jami'in na kasar Uganda, ya kuma bayyana shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da kasar Sin ta gabatar, a matsayin sabuwar hanyar bunkasa tattalin arziki, wadda Afrika za ta iya amfana daga gare ta. Ya ce kamar a galibin kasashen Afrika, kasar Sin ta gina muhimman ababen more rayuwa a bangaren sufuri da makamashi a Uganda, wadanda ke da nufin bude kofar dimbin damarmakin raya tattalin arzikin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China