Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufar Sin na kara taka rawa wajen daidaita gibin kasafin kudi a duniya
2019-12-17 20:19:25        cri

Babban gidan rediyo da talibijin kasar Sin CMG ta ba da wani bayani mai taken "Manufar Sin na kara taka rawa wajen daidaita gibin kasafin kudi a duniya" a yau Talata.

Bayanin ya nuna cewa, jiya Litinin, manyan jami'ai, da masana, da 'yan kasuwa na kasashe fiye da 20, sun halarci dandalin tattaunawa tsakanin kasa da kasa mai jigon "Dangantakar Sin da duniya a sabon karni", inda suka jinjinawa gudunmawar da Sin take bayarwa ta fuskar kasancewar bangarori daban-daban a duniya, da magance matsalar gibin kasafin kudi a duniya.

Bayanin ya kuma ce, ba ma kawai Sin ta fitar da manufofinta a fannnin magance matsalar gibin kasafin kudi ba ne kawai, har ma ta dauki matakai da suka dace. Shawarar "Ziri daya da hanya daya" mataki ne da Sin ta dauka, don ingiza manufar cudanyar bangarori daban-daban a duniya, da hadin kan kasa da kasa bisa tunanin tattaunawa da samun bunkasuwa, da cin moriya tare.

Kazalika, bayanin ya ce, an dora muhimmanci sosai kan goyon bayan kasancewar bangarori daban-daban a duniya, sako mai yakini da taron a wannan karo ya fitar ya kuma ba da tabbaci kan wannan batu.

Nacewa ga tsarin tattaunawa, da samun bunkasuwa, da cin moriya tare, da tsarin sulhuntawa tsakanin al'umomin kasa da kasa, da ingiza kafa tsarin daidaita harkokin duniya bisa adalci, muhimman matakai ne dake cikin manufar Sin, wadda ta ci gaba da taka rawa wajen magance matsalar gibin kasafin kudi a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China