Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG ya bude cibiyarsa dake GBA
2019-11-07 20:15:26        cri
Yau Alhamis 7 ga wata, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin na CMG, ya bude cibiyarsa dake babban yankin mashigin ruwa na Guangdong zuwa Hong Kong zuwa Macao, wato GBA a takaice. A sa'i daya kuma, an fara gabatar da shirye-shiryen "Muryar yankin GBA" ta wayar salula.

Wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana darektan kwamitin jam'iyyar kwamitnis ta kasar Sin na lardin Guangdong Li Xi, ya halarci bikin bude cibiyar, kuma tare da mataimakin ministan harkokin fadakar da jama'a na Kwamitin tsakiyar JKS, kana shugaban CMG Shen Haixiong, su ne suka sanar da budewar cibiyar GBA, da kuma kaddamar da "Muryar yankin GBA" a hukumance. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China