Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude dandalin tattaunawa na "Hanyar Siliki ta ruwa na karni na 21" karo na 3
2019-10-22 21:11:43        cri
Yau Talata aka bude taron dandanlin tattaunawar kafofin watsa labaru na kasa da kasa na "Hanyar Siliki ta ruwa na karni na 21" karo na 3 a birnin Zhuhai na lardin Guangdong na kasar Sin, wanda kafar CMG da gwamnatin lardin Guangdong suka shirya.

A jawabin da ya gabatar wani jami'in CMG Hu Bangsheng ya bayyana cewa, CMG yana goyon bayan raya babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao, yana kuma fatan karfafa hadin kai da kafofin watsa labaru na kasashe daban daban a fannonin kyautata yanayin watsa labaru na kasa da kasa, zurfafa tsarin shirye-shirye, ciyar da hadin kan kafofin watsa labaru da dai sauransu, da nufin more nasarorin da aka samu a yankin, da inganta wadatuwar yankunan dake cikin "Hanyar Siliki ta ruwa na karni na 21".

Wakilin tawagar ofisoshin jakadancin kasashen ketare dake Guangzhou kana karamin jakadan kasar Iran dake Guangzhou, Khalil Shirgholami ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, yana fatan "Hanyar Siliki ta ruwa na karni na 21" za ta kara sada zumunci a tsakanin kasashe daban daban, da inganta hadin kai a tsakaninsu, don karfafa hadin kai da zaman lafiyar duniya. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China