Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG zai zurfafa hadin gwiwa tsakaninsa da kafar watsa labarai ta Golobo ta Brazil
2019-11-13 10:56:01        cri

A ranar 11 ga wata, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da kafar watsa labarai ta Golobo ta kasar Brazil, wato kafar watsa labarai mafi girma a nahiyar Latin Amurka. Bisa wannan yarjejeniya, a nan gaba kadan bangarorin biyu za su habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin shirye-shiryen talabijin, da wasannin motsa jiki, da shirye-shirye masu nishadantarwa, da kuma fasahohin yanar gizo na 5G da dai sauransu.

A wannan rana, mataimakin shugaban sashen fadakar da jama'a na kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban CMG Shen Haixiong, ya gana da takwaransa na kafar watsa labarai ta Golobo Mr. Roberto Marinho Neto a birnin Rio de Janeiro, domin tattauna yadda za a karfafa hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu.

A yayin ganawar tasu, Shen Haixiong ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron kolin kasashen BRICS da za a gudanar a kasar Brazil, lamarin da zai karfafa zumunci da hadin gwiwar tattalin arziki da ta al'adu a tsakanin kasashen biyu. Ya ce ko shakka babu, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Brazil, zai kasance abun koyi ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa.

A nasa bangare kuma, Mr. Roberto Marinho Neto, ya ce, a matsayin babbar kafar watsa labarai mai tasiri ga kasa da kasa, bunkasuwar da CMG ta samu ta burge shi kwarai da gaske. Ya ce yana fatan habaka hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a fannonin shirye-shiryen talabijin, da kara musayar shirye-shirye, da kuma yin amfani da sabbin fasahohi da dai sauransu, tare da kuma karfafa mu'amalar dake tsakanin ma'aikatan bangarorin biyu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China