Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tashar wasanni ta CCTV za ta dakatar da watsa wasannin NBA
2019-10-08 18:43:32        cri

A yau ne, tashar dake watsa wasanni ta CCTV ta babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ta sanar da cewa, za ta dakatar da watsa wasannin kwallon kwando na Amurka (NBA), saboda yadda kwamishinan NBA Adam Silver ya goyi bayan kalamai marasa tushe da babban manajan kungiyar wasan kwallon kwando ta Houston Rockets Daryl Morey ya yi, game da yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Tun a ranar Lahadi ne, babban rukunin CMG, ya yi Allah wadai da kalaman da Daryl Morey ya yi kan halin da ake ciki a yankin na Hong Kong, ya kuma yanke shawarar dakatar da watsa wasannin kungiyar kai tsaye da ake yi, da ma katse duk wata alaka da tuntuba da kungiyar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China