Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a fara watsa shirin talabijin mai taken "bikin murnar ranar haihuwa mafi girma a nan duniya"
2019-11-13 10:31:10        cri
A ranar 13 ga wata, za a fara watsa shirin talabijin na labarai na gaskiya mai taken "bikin murnar ranar haihuwa mafi girma a nan duniya", wanda aka kirkiro cikin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen ketare, ta hanyar gidan talabijin na labarai na gaskiya na CMG, da hanyar talabijin na NGCI na kasar Amurka, da kuma wasu hanyoyin talabijin na wurare da na kamfanoni da dama.

A ranar 12 ga wata, aka yi taron manema labarai game da shirin talabijin mai taken "bikin murnar ranar haihuwa mafi girma a nan duniya" a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Bisa labarin da aka samu, an ce, sashen fadakar da jama'a na kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin ne ya tsara wannan shirin, sa'an nan, cibiyar sadarwa ta kasa da kasa ta CICC, da gidan talabijin na NGCI na kasar Amurka, da kamfanin talabijin da finai-finai na ITV Meridian na kasar Burtaniya suka kirkiri wannan shiri cikin hadin gwiwa, inda suka mai da hankali kan lokacin musamman na cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin, domin maimaita muhimmiyar rawa da kasar Sin ta taka cikn wadannan shekaru 70, da kuma yin hasashe kan makomar kasa mai haske cikin sabon zamani mai zuwa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China