Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG ya kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da kamfanin EBC na Brazil
2019-11-15 10:49:44        cri

A ranar 13 ga watan nan ne, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da kamfanin kafar watsa labarai na kasar Brazil wato EBC a birnin Brasilia, fadar mulkin kasar Brazil. Bisa yarjejeniyar da suka kulla, bangarorin biyu za su fara hadin gwiwa a fannoni daban daban, da za su hada da yin musayar shirye-shiryen talabijin da bidiyo, da tsara shirye-shirye cikin hadin gwiwa, da mu'amalar ma'aikata da kuma fasahohin 5G da dai sauransu.

Shugaban CMG Shen Haixiong, da takwaransa na kamfanin EBC Luiz Gomes, sun kulla wannan yarjejeniya cikin hadin gwiwa. Haka kuma, ministan harkokin jama'ar kasar Brazil da mashawarci jakadan kasar Sin kan harkokin labarai dake kasar Brazil da dai sauransu sun halarci bikin kulla yarjejeniyar.

Cikin jawabinsa, Shen Haixiong ya ce, sabo da goyon baya da shugabannin kasashen biyu suka nuna, ana ci gaba da zurfafa dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Brazil bisa manyan tsare-tsare, har hakan ya zamo abin koyi ga kasashe masu tasowa. Haka kuma, hadin gwiwar dake tsakanin CMG da EBC, zai ta karfafa mu'amala a tsakanin al'ummomin kasashen biyu, kan harkokin al'adu da ma ciniki.

A nasa bangare kuma, Luiz Gomes ya ce, tun daga shekarar 2009, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta ci gaba da kasancewa babbar abokiyar ciniki ga kasar Brazil, ana kuma sa ran cimma sakamako mai kyau, bisa hadin gwiwar dake tsakanin CMG da EBC, kasancewar su manyan kafofin watsa labarai na kasashen biyu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China