Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD tana sa ran karfafa hadin gwiwar aikin gona tsakanin Sin da Afirka
2019-12-17 14:18:34        cri
Jiya Litinin, babban jami'in hukumar kula da harkokin hatsi da aikin gona ta MDD Qu Dongyu ya bayyana yayin taron dandalin matasa na kasa da kasa karo na 3 cewa, a halin yanzu, kasashen Afirka na fuskantar matsalar karancin abinci, a sa'i daya kuma, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a fannin samar da isassun hatsi da aikin gona, don haka, akwai bukatar karfafa hadin gwiwa a fannin aikin gona tsakanin Sin da Afirka

Daga ranar 14 zuwa ranar 17 ga wata, aka gudanar da taron dandalin matasa na kasa da kasa karo na uku a birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar, Qu Dongyu ya halarci taron samar da isasshen hatsi a kasashen Afirka da taron samun dauwamammen ci gaba.

Qu Dongyu ya ce, kasashen Afirka da yankin gabashin bahar Rum sun shafe shekaru sama da goma suna fama da karancin abinci, wannan babban kalubale da ya shafi duniya baki daya.

Haka kuma, ya ce, raya harkokin yanar gizo, kirkire-kirkire da zuba jari su ne manyan hanyoyin warware wannan matsala, don haka, ya kamata matasa su kara shiga aikin gona, da kuma dukufa wajen samar da sabbin fasahohi a wannan fanni.

Ya ce, a watan Satumba na bana, hukumar abinci da aikin gona ta MDD ta yi "kira da a hada hannu", inda ta sa kaimi ga kasashe masu ci gaba da su hada kai da kasashe maras ci gaba, domin kafa dandalin musayar muhimman bayanai da kasuwanni da kirkire-kiekire.

Ya ce, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a fannin samar da isassshen abinci da aikin gona, ta samar da isasshen abinci ga kaso 22 na al'ummar duniya, da gonakin da ya kai kaso 7 kawai na fadin gonakin duniya, bisa manufofin kirkire-kirkire da suka dace. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China