Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta warware matsalar abinci da ta damu 'yan kasar kimanin biliyan 1.4
2019-10-15 14:22:13        cri

Jiya ranar 14 ga wata, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani kan wadatar abinci. Wannan shi ne irin takardar ta biyu da gwamnatin kasar ta bayar tun bayan shekarar 1996. Takardar ta nuna cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, kasar ta samu manyan nasarori a fannin wadatar abinci, wadanda suka ba duniya mamaki sosai. Ban da wannan kuma, Sin ta kara bude kasuwar hatsinta ga duniya, da sa kaimi ga ci gaban cinikayyar hatsi tsakanin kasa da kasa, da ma fadada dangantakarta da kasashen waje a wannan fanni, da kuma yin kokari don ganin an kawar da matsalar yunwa a duk duniya baki daya. Lamarin da ya sa Sin ta bayar da muhimmiyar gudummawa a wannan fannin.

Zhang Wufeng, shugaban hukumar ajiyar hatsi da kayayyaki ta kasar Sin ya bayyana jiya a birnin Beijing cewar, tun bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, ko da yaushe Sin na sanya batun fama da yunwa a gaban dukkan ayyukan tafiyar da harkokin kasa. Bisa yawan kididdigar da aka yi, takardar bayani kan wadatar abinci ta shaida cewa, ko da yake kasar Sin tana da tushe maras inganci a fannin ayyukan gona kuma jama'arta na fama da talauci a farkon kafuwarta, amma a karkashin jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Sin ta cimma nasarar samar da isasshen abinci bisa namijin kokarin da take yi. Ba warware matsalar abincin da ta damu jama'arta kimanin biliyan 1.4 kadai ta yi ba, har ma da kyautata zaman rayuwar al'ummarta. Lallai ta samu manyan nasarorin da suka ba duniya mamaki sosai a wannan fannin. Zhang yana mai cewa,

"Bisa gonakin da yawansu ya kai kaso 9% na duniya da ma albarkatun ruwan sha da yawansu ya kai kaso 6% na duniya, kasarmu ta ciyar da mutanen da yawansu ya kai kusan kaso 20% na al'ummar duniya, har ma ta samu babban sauyi daga matakin fama da yunwa zuwa na samun isasshen abinci har zuwa matakin yanzu na samun wadatar abinci. Lamarin da ya sa ba kawai samar wa kanta isasshen abinci Sin ta yi ba, har ma da bada gudummawa wajen kawar da yunwa a duniya baki daya."

A cikin takardar bayanin kuma, an bayyana yadda kasar Sin ke bude kofarta ga ketare da ma hadin kanta da kasashen duniya a fannin wadatar abinci. Zhang Wufeng ya furta cewa, takardar bayanin ta nuna yadda Sin ke sauke nauyin dake kanta a fannin yin kokarin don ganin an kawar da matsalar yunwa a duniya baki daya, bisa matsayinta ta wata babbar kasa. Zhang ya kara da cewa,

"Gwamnatin Sin na martaba ka'idar yin cinikayya cikin 'yanci da kokarin cika alkawarin da ta yi yayin da ta shiga kungiyar cinikayya ta duniya ta WTO, domin sa kaimi wajen samun wadatar abinci a duniya. A wani bangare, Sin na inganta bude kofarta a wannan fannin. Alal misali, ta soke tsarin kayyade aikin shigo da amfanin gona da dai sauran matakan da suke da alaka da harajin kwastam, da ma sassauta kayyade zuba jarin da 'yan kasuwa na ketare ke yi a fannin aikin gona, hakan ya sa kamfanonin ketare na iya raya ayyukansu sosai a kasuwar hatsin Sin. A dayan bangaren kuma, Sin na habaka hadin kai da kasa da kasa. Bisa manufar 'kulla dangantaka bisa gaskiya da kauna da yarda da aminci' da kuma dabarar 'cimma muradu da kuma martaba ka'idoji', kasar Sin na nuna himma da kwazo a cikin aikin samar da wadatar abinci a duniya da ma samar da taimakon hatsi cikin gaggawa gwargwadon karfinta, bisa tsarin raya shawarar 'ziri daya da hanya daya', da dandalin FOCAC, da tsarin hadin kan kasashe masu tasowa."

A ganin Manazarci Li Guoxiang na cibiyar nazarin raya yankunan karkara ta kwalejin nazarin kimiyyar zaman takewar al'ummar kasar Sin, yanzu Sin na kara bude kasuwarta ta hatsi. Li ya ce,

"kasashe da dama na fatan kasar Sin za ta kara bude kasuwar amfanin gonanta, hakika dai Sin na cika alkawuranta na kara bude kofa ga waje. Game da hatsin da Sin ta samar, ana iya sayen akasarin ire-irensu a kasuwannin duniya. Game da amfanin gona da ake shigowa da su, tun bayan da Sin ta shiga WTO, ta rage yawan harajin kwastam sosai da take karba, haka kuma ta soke tsarin duba amfanin gona don ba da iznin shigowa, lamarin da ya sa aikin gona ke iya dacewa da ci gaban cinikayya cikin 'yanci sosai."

Takardar bayanin ta kuma bayyana cewa, Sin da sauran manyan kasashe masu samar da hatsi na raya kasuwar duniya tare. A shekarar 2018, Sin ta shigo da hatsi fiye da tan miliyan 20 da wake fiye da tan miliyan 80, lamarin da ya kara azama ga bunkasar cinikayyar hatsi a duk fadin duniya.

Mataimakin babban sakataren kwamitin raya kasa da yin gyare-gyare na Sin Su Wei ya yi tsokaci cewa, Sin na son more sakamako da musanyar fasahohi da ayyukan gona tare da kasashe daban daban, da himmatuwa wajen kawar da yunwa a duniya, da ma kiyaye ka'idojin WTO, a kokarin samun wadatar abinci a duk duniya baki daya.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China