Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afirka na bukatar sabbin dabarun dakile kalubalen yunwa da karancin abinci, in ji wani jamii
2019-11-27 11:04:56        cri

Firaministan kasar Rwanda Edouard Ngirente, ya ce nahiyar Afirka na bukatar aiwatar da sabbin dabaru, don dakile kalubalen yunwa da karancin abinci dake addabar wasu sassan ta.

Mr. Ngirente ya yi wannan tsokaci ne, yayin kaddamar da taron kolin dandalin shirin samar da abinci na Afirka wato "African Green Revolution Forum" ko AGRF na shekarar 2020. Karkashin wannan dandali da zai gudana a badi, ana fatan tattauna muhimman batutuwan da suka jibanci yunwa da kamfar abinci a Afirka.

Firaministan dake tsokaci a birnin Kigalin kasar Rwanda, ya ce wadannan kalubale na shafar rayuwar miliyoyin al'ummun nahiyar Afirka, don haka lokaci yayi da za a zakulo sabbin dabarun samar da isasshen abinci, da fatattakar yunwa baki daya. Ya ce kasashen nahiyar na bukatar karfafa ayyukan malaman gona, su kuma tabbatar da cewa manoma na samun kayan aiki a kan lokaci, musamman irin shuka mai nagarta, da takin zamani, don cimma nasarar da aka sanya gaba.

Ana dai sa ran gudanar da wannan dandali na tattauna hanyoyin inganta noma a Afirka tsakanin ranekun 8 zuwa 11 ga watan Satumbar badi, domin jan hankalin mahukunta, da sauran masu ruwa da tsaki, ta yadda za a fitar da managartan manufofi, da dabarun zuba jari, har a kai ga samar da ci gaba mai dorewa a daukacin fannonin noma a nahiyar baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China