Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afrika su magance matsalar asarar amfanin gona bayan girbi domin bunkasa wadatuwar abinci
2019-09-15 15:43:06        cri

Tarayyar Afrika AU, ta bukaci kasashen Afrika da sauran hukumomin kasa da kasa na nahiyar, su hada karfi don magance matsalar asara da bata amfanin gona bayan girbi, domin tabbatar da wadatuwar abinci a nahiyar.

Tarayyar ta ce, nahiyar Afrika ce ta fi fuskantar matsalar karancin abinci a duniya, inda ta yi kiyasin 1 cikin mutane 4 a nahiyar na fama da karancin sinadaran gina jiki, ta alakanta matsalar da asarar amfanin gona mai yawa bayan girbi a kasashen dake fadin nahiyar.

Alkaluma daga AU sun nuna cewa, jimilar abun da ake asara a nahiyar ya kai sama da metric ton miliyan 100 a kowacce shekara, yayin da asarar da ake a duniya baki daya, ya tsaya kan metric ton biliyan 1.3, kwatankwacin sama da kaso 30 na jimilar abincin da ake samarwa domin amfanin bil adama, kana ta yi kiyasin yawan abincin da ake asara a duniya, zai iya ciyar da mutane biliyan 1.6 a kowacce shekara.

Ta ce, wannan asarar na ta'azzara karancin abinci da yin mummunan tasiri kan muhalli ta hanyar lalata ban kasa da ruwa da kayayyakin gona da karfin da aka sa wajen samar da abincin da ba a yi amfani da shi ba.

AU ta jaddada cewa, asarar bayan girbi na rage kudin shigar manoma tare da ba da gudunmuwa ga hauhawar farashin kayayyakin abinci.

Kiran na rage asara da bata amfanin gona da Tarayyar ta yi, na zuwa ne gabanin taron bayan girbi da baje koli karo na 2 na nahiyar, da za a yi daga ranar 17 zuwa 20 ga wata, a hedkwatar AU dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China