Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya ya yi kira da a kara samar da abinci don kawar da talauci
2019-09-17 09:44:40        cri

Wani sabon rahoto da babban bankin duniya ya fitar a jiya Litinin, ya bayyana bukatar da ke akwai ga kasashe masu tasowa, da su kara yin kirkire-kirkire a fannin aikin gona da ma kara yawan abincin da suke samarwa, a wani mataki na kawar da matsalar kangin talauci da jure tasirin sauyin yanayi.

Rahoton ya ce, kaso biyu bisa uku na masu fama da kangin talauci, sun dogara ne ga aikin gona, kuma karuwar abincin da ake samarwa, tana yin babban tasiri kan kowane bangare na kawar da talauci.

Rahoton ya kara da cewa, yayin da karuwar abincin da ake samarwa a kasar Sin da sauran kasashen dake gabashin Asiya ta yi tasiri wajen kawar da talauci, a hannu guda kuma, lamarin ya yi karanci matuka a nahiyar Afirka da yankin kudancin Asiya, inda har yanzu ake fama da kangin talauci.

Mataimakin shugaban bankin duniya mai kula da daidaiton ci gaba, harkokin kudi da hukumomi Ceyla Pazarbasioglu, ya bayyana cewa, inganta bangaren aikin gona, zai taimaka matuka wajen samar da ayyukan yi masu kyau, yayin da karin al'ummu za su kaura zuwa birane don neman wasu damammaki.

Taken rahoton shi ne, "makomar girbin amfanin gona: fasahar zamani da kara samar da abinci a bangaren aikin gona". (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China