Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin nune nunen abinci na kasar Sin zai taimaka wajen rage talauci
2019-09-14 17:02:24        cri
Za a kaddamar da bikin nune-nunen abinci karo na 20 na kasar Sin, a Nanchang, babban birnin lardin Jiangxi na gabashin kasar Sin, daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Nuwamba, wanda kuma ke da nufin taimakawa yankuna masu talauci bunkasa kudin shiga ta hanyar baje kayayyakin abinci da sayensu.

Daraktan kungiyar masu gidan sayar da abinci ta kasar Sin, Han Ming, ya ce galibin kayayyakin da ake bukata na sarrafawa a sana'ar sayar da abinci, albarkatu ne na gona, kuma sayen wadannan kayayyakin da yawa daga yankunan masu fama da talauci, zai taimaka sosai wajen bunkasa kudin shigar manoman yankunan.

Yayin bikin, za a daukewa masu baje kolin kayayyaki daga yankuna masu talauci kudin da ake biya. Kuma mashirya bikin, za su samar da damarmaki ga kamfanoni masu sana'ar sayar da abinci ta hanyar tattaunawar kasuwanci.

Har ila yau yayin bikin, za a gudanar da taro kan ingancin harkar sayar da abinci, inda za a tattauna kan maudu'ai da suka hada da irin yayin da zai zo a nan gaba da sabbin tsarukan kasuwanci da kula da hidimar samar da kayayyaki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China