Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gana da Carrie Lam Cheng Yuet-ngor a birnin Beijing
2019-12-16 20:22:29        cri

Da yammacin yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da kantomar yankin Hong Kong Carrie Lam Cheng Yuet-ngor a nan birnin Beijing, inda ya saurari rahoton aikinta, da ma halin da yankin ke ciki.

Xi Jinping ya ce, a cikin wannan shekara dake daf da kammala, yankin Hong Kong ya fi fuskanci mawuyancin hali tun bayan da ya dawo da hannun babban yankin. Kaza lika gwamnatin tsakiya ta amince da aikin da Carrie Lam Cheng Yuet-ngor ke gudanawa.

A cewarsa, ran 14 ga watan Nuwamba da ya gabata, ya halarci taron koli karo na 11 na BRICS da aka yi a Brazil, kuma ya ba da jawabi, inda ya bayyana matsayin da gwamnatin tsakiya ke dauka kan batun Hong Kong. Ya ce niyyar kasar Sin na tabbatar da ikon mulkin kasa, da tsaron kasar, da kuma cimma muradun ci gaban kasa, ko kadan ba za su canja ba, kuma za ta nace ga manufar "Kasa daya mai aiwatar da tsarin mulki biyu", da kin yarda da kowane karfi na ketare ya tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar ta Sin.

Xi Jinping ya kara da cewa, gwamnatin tsakiya za ta ci gaba da goyon bayan Carrie Lam Cheng Yuet-ngor, ta yadda za ta jagoranci gwamnatin yankin Hong Kong, don aiwatar da harkokin yankin bisa doka da shari'a, da kuma ci gaba da mara baya ga 'yan sandan yankin, da goyon bayan masu kishin kasa da masu kaunar Hong Kong. Har ila yau kuma, ya yi fatan al'umomin yankin za su yi hadin kai don maido da Hong Kong kan hanyar da ta dace.

Ban da wannan kuma, firaministan kasar Sin Li Keqiang shi ma ya gana da Carrie Lam Cheng Yuet-ngor a wannan rana.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China