Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya gana da wakilan kasashen waje da suka halarci taron dandalin hadin gwiwa da musaya na kasa da kasa
2019-12-04 09:32:47        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga kasashen duniya, da su sauke nauyin dake bisa wuyansu, da tuntubar juna da neman hanyar warware bambance-bambancen dake tsakaninsu,da martaba alakar kasa da kasa don gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam.

Xi ya bayyana haka ne, yayin da yake ganawa da wakilan kasashen waje da suka halarci taron dandalin hadin gwiwa da musaya na kasa da kasa da aka gudanar daga ranar 1-2 ga watan Disamban wannan shekara a birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake yankin kudancin kasar Sin.

Shugaba Xi ya ce, har kullum kasar Sin na da ra'ayin cewa, al'ummomin kasashe daban-daban na da 'yancin zabar hanyar raya kasa da ta dace da yanayin kasashensu. Sannan ba ta goyon bayan tsarin nuna danniya da wasu dake kiran kansa manyan kasashe ke yi. Yana mai cewa, tarihi da al'adun kasar Sin na shekaru 5,000 sun tabbatar da ra'ayin neman 'yanci cikin lumana.

Ya bayyana cewa, kasar Sin ta himmatu wajen tabbatar da daidaito da cin moriya tare a tsarin alakar kasa da kasa, da kara fahimtar juna da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna da dukkan kasashe, ta yadda za a gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China