Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya aike da wasikar taya murna ga taron musaya da tuntuba na manyan jami'an Sin da Japan
2019-11-25 13:57:22        cri

Shugaban kasar Sin, Xi Jinping da takwaransa na Japan, Shinzo Abe, sun aike da wasikun taya murna ga taro karo na farko, na manyan jami'an Sin da Japan, kan musaya da tuntuba tsakanin al'ummomi, wanda ke gudana a birnin Tokyo.

Xi Jinping ya yi bayani cewa, Sin da Japan na da zirin ruwa da tarihi iri guda. Kuma a yanzu, dangantaka tsakanin kasashen na ci gaba da kyautata. Yana mai fatan Sin da Japan za su yi amfani da wannan dama su inganta musaya da hulda tsakanin al'ummominsu da ba da goyon baya wajen raya dangantakar da za su cimma bukatun sabon zamani.

A tasa wasikar taya murnar, Shinzo Abe, ya ce tsarin tuntuba da musaya tsakanin manyan jami'an kasashen 2 matsaya ce da aka cimma yayin ganawarsa da shugaba Xi Jinping a birnin Osaka, wadda ke da nufin zurfafa fahimtar juna da abota tsakanin al'ummomin kasashen biyu ta hanyar zurfafa musaya. Ya kuma yi fatan wannan tsari zai karfafa tubulin ra'ayin jama'a game da gina dangantaka tsakanin kasashen, ta yadda zai dace da sabon zamanin da ake ciki da kuma ba da gudunmuwa ga samar da sabuwar makoma ga dangantakar Sin da Japan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China