Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gana da shugabar IMF
2019-11-22 14:10:41        cri
Yau Jumma'a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar asusun ba da lamuni ta IMF Kristalina Georgieva a babban dakin taron jama'ar kasar Sin.

A yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana adawa da ra'ayin kariyar ciniki domin kiyaye tsarin cinikin dake tsakanin kasa da kasa, wanda kungiyar cinikayya ta duniya ta WTO ta tsara. Kana, kasar Sin tana fatan asusun IMF zai ci gaba da ba da gudummawa cikin harkokin ciniki na kasa da kasa, da kiyaye adalci a kasuwannin hada-hadar kudi na kasa da kasa, ta yadda za a inganta yanayin adalci da daidaito a tsarin kasa da kasa. Kuma kasar Sin tana son ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kungiyar IMF.

Xi ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta tsayawa tsayin daka kan sabbin manufofin raya kasa, domin inganta bunkasuwar tattalin arziki, da kara bude kofa ga waje, ta yadda Sin za ta samar da karin damammaki ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Ya ce, tabbas, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da bunkasa cikin yanayi mai kyau.

A nata bangare kuma, Kristalina Georgieva ta ce, a shekara mai zuwa, kasar Sin za ta kawar da talaucin al'ummomin kasar gaba daya, wannan aiki na da muhimmiyar ma'ana ga kasa da kasa. Bisa kwaskwarimar da kasar Sin ta yi a gida da ma yadda take bude kofarta ga kasashen ketare, ta tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin kasar, kuma ta yi imanin cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga kasa da kasa a fannonin hada-hadar kudi, zuba jari da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China