Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya gana da tsohon sakataren wajen Amurka
2019-11-22 20:25:14        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da tsohon sakataren wajen Amurka Henry Kissinger a Juma'ar nan. A yayin ganawar ta su, shugaba Xi ya yiwa Kissinger fatan karin tsawon shekaru cikin koshin lafiya, yana mai burin ganin tsohon jami'in na Amurka, ya ci gaba da yayata manufar kyautata alakar Sin da Amurka.

Shugaban na Sin, ya ce, a halin yanzu, yanayin alakar Sin da Amurka na cikin wani yanayi mai cike da wahalhalu da kalubale, don haka ya bukaci kasashen biyu da su ci gaba da tattaunawa game da muhimman batutuwa, su kaucewa sabani, da yiwa juna mummunan zato, su kuma kara inganta fahimtar juna.

Ya ce ya kamata sassan biyu, su dauki matakan da za su haifar musu moriya a tsakanin su, da ma sauran sassan duniya baki daya. Kuma akwai bukatar su martaba juna, su dauki matakan bai daya, tare da fahimtar sabanin dake tsakanin su. Su rungumi matakai da za su haifar da cin moriyar juna yayin hadin gwiwa, da bunkasa alakar ci gaba a kan tafarki madaidaici.

Shi kuwa a nasa bangare, Mr. Kissinger cewa ya yi, cikin shekaru 50 da suka gabata, ya ziyarci kasar Sin kusan sau 100, ya kuma ganewa idanun sa irin manyan sauye sauye da kasar ta samu. A hannu guda kuma duk da fadi-tashi da aka fuskanta, alakar Sin da Amurka na ci gaba da bunkasa tsawon wadannan shekaru.

Kissinger ya ce a yanzu, duniya ta sauya matuka, kuma muhimmancin alakar Sin da Amurka na kara fitowa fili. Daga nan sai ya gabatar da shawarar karfafa tattaunawa tsakanin sassan biyu, da aiki tukuru wajen zakulo hanyoyin warware banbance banbance, da fadada hadin gwiwar sassa daban daban, mataki da a cewar sa zai yi tasiri matuka ga ci gaban kasashen biyu, da ma sauran kasashen duniya baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China