Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A karon farko Sin ta gabatar da kyawawan tamburan kamfanonin kasar na shekarar 2019
2019-12-16 11:08:36        cri

Jiya Lahadi, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG ya yi bikin kyawawan tamburan kamfanonin kasar Sin na shekarar 2019 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A yayin bikin, karon farko an gabatar da kyawawan tamburan kamfanonin kasar Sin, wakilan kamfanoni sama da dari daya sun halarci wannan biki.

Mataimakin shugaban sashen fadakar da jama'a na kwamitin tsakiyar JKS, kana shugaban CMG Shen Haixiong ya halarci wannan biki, tare da ba da lambobin yabo ga kamfanonin da suka samar da tambura masu kyau da inganci

Bugu da kari, a yayin bikin, an ba da lambobin yabo ga tambura 100 dake zama abin koyi, da lambobin yabo na "manyan tambura guda 10 na shekarar 2019", da lambobin yabo na sabbin tambura masu inganci guda 10 na shekarar 2019, da kuma lambar yabo ta tambari da ya fi fice na shekarar 2019.

Kamfanin Huawei ya lashe lambar tambari da ya fi fice na shekarar 2019, saboda kokarin da ya yi a fannin kirkire-kirkire, da kuma nasarar da ya samu wajen raya fasahar yanar gizo ta 5G da matsayinsa na zama a kan gaba a duniya, ta yadda ya sa tambarin wayar salula na Sin ta shiga jerin tamburan wayar salula masu kyau da inganci na kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China