Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana mai da hankali kan kyautata zaman rayuwar al'umma yayin da take neman ci gaban kasa, in ji jami'in Madagascar
2019-12-12 14:12:10        cri
A yayin taron dandalin tattaunawar hakkin dan Adam na kasashe masu tasowa na shekarar 2019 da aka yi a birnin Beijing tsakanin ranekun 10 zuwa 11 ga wata, mataimakin shugaban majalisar dattijan kasar Madagascar, kana tsohon firaministan kasar Kolo Christophe Laurent Roger ya bayyana cewa, ainihin burin ci gaban kasa shi ne al'ummomin kasa su samu damar jin dadin zaman rayuwarsu, kuma kasar Sin ta kan mai da hankali wajen kyautata zaman rayuwar jama'arta a lokacin da take neman bunkasuwar kasa baki daya.

Malam Roger ya kara da cewa, ta hanyar halartar wannan taro da wasu bukukuwa masu nasaba da shi, ya sami damar ganewa idanunsa irin bunkasuwar kasar Sin. Kuma dukkanin tsare-tsaren siyasa akwai kwarewa a cikinsu. Har ila yau kasar Sin ta samu wata hanyar neman bunkasuwa, wadda ta dace sosai da halin da take ciki. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China