Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala taron dandalin tattaunawar hakkin Bil Adama na kasashe masu tasowa na shekarar 2019
2019-12-12 16:30:10        cri

An kammala dandalin tattaunawar batun hakkin Bil Adama na kasashe masu tasowa na shekarar 2019 a nan birnin Beijing, wanda ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin suka shirya cikin hadin kai.

A cikin wannan taron dandali na kwanaki biyu, wakilai daga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 300, sun tattauna kan taken "Kasancewar al'adu iri daban daban na duniya, da bunkasuwar hakkin Bil Adama" tare da kaiwa ga matsaya daya, wanda ke kunshe da manyan batutuwa hudu, ciki hadda "Hanyar kare Bil Adama da za a zabi karkashin kasancewar al'adu iri daban-daban a duniya", da "raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya, da daidaita batun hakkin Bil Adama a duniya", da kuma "Hange daga hakkin samun bunkasuwa: Shawarar 'Ziri daya da hanya daya' za ta ingiza samun bunkasuwa mai dorewa na shekarar 2030", kana da "Fasaha da darasin kasashe masu tasowa kan kare hakkin Bil Adama." (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China