2019-12-13 10:33:37 cri |
Haka kuma, ya ce, ba kawai batun jihar Xinjiang yana shafar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Sin ba ne, har ma yana da muhimmanci ga zaman lafiya da zaman karko na yankin baki daya. Ya ce, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan yaki da ta'addanci a jihar Xinjiang, domin kiyaye zaman karko da zaman lafiyar kasar kanta, tana kuma ba da gudummawa wajen kiyeye zaman lafiyar yankin baki daya.
Dokar hakkin dan Adam kan jihar Xinjiang ta kasar Sin da majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas, ta zama lamarin tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, ta kuma bata sunan kasar Sin, a wani yunkuri na hura wutar rikici a kasar. Kazalika an samar da wannan doka ne bisa dalilai na siyasa, ba bisa dalili na doka ba, wanda hakan ya kasance wata hujja ta kasar Amurka, wadda ta kan yi amfani da ita wajen tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe. (Maryam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China