Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mahalartar taron kasashe masu tasowa game da hakkin dan-Adam sun yi na'am da matakan Sin na tabbatar da zaman lafiya a Xinjiang
2019-12-12 19:19:35        cri

Wakilan da suka halarci taron dandalin kasashe masu tasowa game da kare hakkin dan-Adam da ya gudana daga ranar 10 zuwa 11 ga wata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, sun shaidawa manema labaran babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG cewa, kasar Sin ta samu sakamako mai gamsarwa a fannin kare hakkin dam-Adam a yankin Xinjiang, tare da yin na'am da matakan tabbatar da zaman lafiya da mahukuntan kasar suka dauka a yankin na Xinjiang.

A zantawarsa da manema labarai, tsohon shugaban hukumar kare hakkin dan-Adam na Jamhuriyar Nijar, Halid Ikhiri ya bayyana ta'addanci a matsayin babban makiyin al'ummar Nijar, yana mai cewa, a matsayinta na kasar dake yankin Sahara, Nijar ta sha wahala matuka. Ta'addanci ya kawo cikas ga ci gaban galibin kasashe matalauta a duniya.

Ya ce, yankin Xinjiang ya kasance fagen daga na yaki da 'yan ta'adda a kasar Sin. Don haka ya zama wajibi a hada kai don ganin bayan ayyukan ta'addanci a yankin na Xinjiang.

Da ya juya ga batun "Dokar nan ta kare hakkin dan-Adam ta Uygur ta shekarar 2019" da majalisar wakilan Amurka ta zartas, Ionel Vairon, wani masanin kasar Faransa dake Luxemburg, ya bayyana cewa, dokar ta nuna ra'ayin kama karya na Amurka a harkokin kasa da kasa da na shiyya.

Ya ce, dokar "neman fakewa ne" da Amurka ke yi don ta matsawa kasar Sin lamba da ma shiga harkokin cikin gidanta ta hanyar amfani da batutuwan da suka shafi kare hakkin bil-Adama.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China