Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin watsa labaran kasashe yammacin duniya sun yi shiri kan batun Xinjiang
2019-12-09 20:02:52        cri

Kwanan baya gidan talabijin na kasa da kasa na kasar Sin wato CGTN a takaice ya nuna wasu shirye-shiryen bidiyo guda biyu kan ayyukan yaki da ta'addancin da ake yi a yankin Xinjiang na kasar Sin cikin harshen Turanci, inda aka yi cikakken bayani kan kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi domin yaki da ta'addanci a yankin ta hanyar gabatar da hakikanin abubuwan da suka faru, kana an bayyana cewa, dakarun kungiyar 'yan ta'adda ta gabashin Turkiyya ETIM suna yada tsattsauran ra'ayi tare kuma da aikata laifuffukan ta'addanci a yankin, amma manyan kafofin watsa labaran kasashe yammacin duniya wadanda suke mai da hankali kan batun yankin Xinjiang sun yi shiru, ba su kuma ce komai ba kan wadancan shirye-shieyen bidiyon da aka gabatar.

Yau Litinin kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, "Ina so in jaddada cewa, ko ku gabatar da labarai, ko ba ku so ku gabatar da labarai, wannan ba zai taimaka da komai ba, saboda mun gabatar da ainihin abubuwan da suka faru a yankin, ya kamata kafofin watsa labarai su sauke nauyi dake bisa wuyansu su gabatar da labarai ga jama'a bisa adalci, bai kamata ba su zabi abubuwan da suke bukata domin jama'a su goyi bayansu".(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China