Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafar yada labarai ta Nijeriya: Gwano ba ya jin warin jikinsa
2019-12-10 10:13:09        cri

A jiya Litinin ne babban editan jaridar "Nigerian Pilot" Austin Maho ya fitar da wani sharhi, inda ya jinjinawa manufofin da Sin ta dauka wajen yaki da ta'addanci a jihar Xinjiang, tare da yin tir da fuska biyu, da kuma munafurcin Amurka kan batun yaki da ta'addanci da kare hakkin Bil Adama.

Sharhin ya nuna cewa, Sin ta kafa cibiyoyin horar da fasahohin sana'o'i a jihar Xinjiang, a matsayin matakin da ya dace wajen yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi, da ingiza hadewar al'umma waje guda, wanda ya zama abin koyi ga sauran kasashe wadanda tsattsauran ra'ayi da ta'addanci ke dabaibaye su matuka. Amma, wasu kasashen yamma musamman ma Amurka, ba sa yi la'akari da mulkin kan kasar Sin na tabbatar tsaronta, maimakon haka ta illata abun da yake na gaskiya, ta nuna bambancin ra'ayi kan hakkin Bil Adama. Abin ban dariya shi ne, Amurka ta dade tana yin suka kan sauran kasashe, amma sa'i daya kuma, matsalar hakkin Bil Adama dake aukuwa a kasar ta yi kamar ba su gani ba su ji ba. Alal misali, a wurin tsare makaurata a Amurka, an tilasta dubban yaran makaurata da su rabu da iyayensu, an tsare daruruwan mutane a gidan kurkuku na Guantánamo ba tare da yin musu hukunci ba, har ma ana azabtar da su. Ya zuwa karshen watan Maris na bana, mai ba da rahoto na musamman na MDD, ya ba da takardu guda 22 don neman amsa daga Amurka kan batun hakkin Bil Adama. Amma game da wannan batu, Amurka ta yi tamkar ta makance ba tare da ba da kowane martani ba. Amurka mai fuska biyu kan batun hakkin Bil Adama, na kaunar fakewa da wannan batu don takalar sauran kasashe, babu wani nufi da take da shi sai shisshigi cikin harkokin gidan sauran kasashe, tamkar dai gwano ne da ba ya jin warin jikinsa, amma ba zai iya boye warin jikinsa ko kadan ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China