Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban gwamnatin jihar Xinjiang: Bai kamata Amurka ta yi fuska biyu kan aikin yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi ba
2019-12-09 13:35:23        cri

Mataimakin direktan kwamitin reshen jihar Xinjiang ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban gwamnatin jihar, Shohrat Zakir, ya bayyana a gun taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya, cewar kwanan baya, majalisar wakilan Amurka ta zartas da doka, wato wai dokar hakkin Bil Adama na Uygur na shekarar 2019, abun da ya keta dokar kasa da kasa, da ka'ida mai tushe ta dangantakar kasa da kasa, wanda hakan shisshigi ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin.

Ya ce matakan da Xinjiang ke dauka na yaki da ta'addanci da kawar da tsttsauran ra'ayi, iri daya ne da wadanda sauran kasashe a duniya ke dauka, ciki hadda Amurka.

Yana mai cewa, Xinjiang na bunkasuwa cikin wadata mai dorewa, kuma al'umomin jihar na hadin kansu yadda ya kamata, ba kuma wanda zai hana hakan. A shekarun baya-baya, GDPn jihar ya karu da kashi kimanin 8.5 cikin dari a ko wace shekara, kuma yawan kudin shiga na mazaunan jihar ya karu da sama da kashi 8 cikin dari a kowace shekara. Ban da wannan kuma, yawan masu shakatawa da jihar ta karbi a shekarar 2018 ya kai miliyan 1150, adadin da ya karu da kashi 40.1 cikin dari bisa na makamancin lokaci na 2017. Haka zalika, a watannin 10 da suka gabata na shekarar bana, wannan adadi ya haura miliyan 200, wanda ya karu da kashi 42.6 ciki dari bisa na bara. Ban da wannan kuma, yawan mutanen da aka kubutar da su daga kangin talauci ya kai fiye da miliyan 2. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China