Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fina-finai game da yaki da ta'addanci a jihar Xinjiang sun janyo hankulan 'yan kasar Iran
2019-12-11 13:25:19        cri

Kwanan baya, gidan telabijin na kasa da kasa na kasar Sin CGTN ya gabatar da fina finai biyu game da yaki da ta'addanci a jihar Xinjiang ta kasar Sin. Fina-finan sun bayyana labarai na Turanci kan yanayin ta'addanci mai tsanani a jihar Xinjiang, da matakan da ya kamata gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen yaki da 'yan ta'adda, da yin cikakken bayani kan me ya sa aikin "kawar da tsattsauran ra'ayi" ya zama hanyar kadai da za a iya shimfida zaman lafiya na dindindin a jihar.

Fina-finan sun janyo hankulan kafofin watsa labarai na kasar Iran kwarai da gaske. Wani dan kasar Iran da ya kalli fina-finan ta yanar gizo ya yi Allah wadai da kakkausar harshe kan yadda 'yan ta'adda suka koyar da yara tsattsauran ra'ayi, ya kuma nuna adawa da kasar Amurka da wasu kasashen yammacin duniya domin fuska biyu da suka yi kan batun yaki da ta'addanci a jihar Xinjiang.

Haka kuma, ta shafinsa na FACEBOOK, wani dan kasar Iran ya nuna yabo matuka kan babban ci gaba da jihar Xinjiang ta samu cikin 'yan shekarun nan. A sa'i daya kuma, ya nuna fahimta kan matakan yaki da ta'addanci da gwamnatin kasar Sin ta dauka, ya ce, a ganinsa, Sin ta cimma nasarar aiwatar da wadannan matakai. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China